Kasashen Duniya Sun yi Tir Da Matakin Da Isra’la Ta Dauka Kan Tawagar Sumud Flotilla.

Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla  ajiya

Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla  ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza.

Haka zalika shugaban kasar Bolivia da takwaransa na kasar Cuba  suna yi Allah wadai da Isra’ila , haka su ma ministocin harkokin wajen spaniya jose manueal dana kasar irish simon harris sun bayyana damuwarsu matuka game da halin da tawagar ta flotilla ke ciki a hannun Israi’la na kokarin hana su isa yankin gaza.

Ita dai tawagar Sumud Flotilla tana dauke da magunguna da abinci da sauran kayan Agaji, kuma ta kunshi jiragen ruwa akalla guda 40 dake dauke da yan majalisa da lauyoyi da sauran masu  rajin kare hakkin dan Adam guda 500, itace tawaga mai karfi dake nuna adawa da killace gaza da HKI ta yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted