Kasashen Duniya Sun Yi Ta AiIka Tallafi Bayan Fashewar Bandar Abbas

Ana kara samun karin ta’aziyya da kuma tallafa daga kasashen waje bayan fashewar da ta auku a tasahr jiragen ruwa na Dr Rajai a Bandar

Ana kara samun karin ta’aziyya da kuma tallafa daga kasashen waje bayan fashewar da ta auku a tasahr jiragen ruwa na Dr Rajai a Bandar Abbasa.

Tashar talabijin ta Press Tv ta nakalto ministan harkokin cikin gida Eskandar mumunina yana fadar haka, yana kuma cewa ya zuwa yanzu, mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu a yaynda wasu a yayinda wasu tsakanin 700-750 suka ji rauni.

Tankar dakon mai ce ta yi binda a cikin tashar jiragen ruwan, a jiya, ammam ba’a san musabbin fashewar ba hanyanzu. Wuta ta kona tankar ta kuma tsallaka zuwa wasu kayaki kusa da wurin.

Sannan bindigan da tankar ta tayi ya watsa wutar zuwa wasu wurare daga nesa, ya fasa gilashan mutocin da suke gewaue, da wasu gine-gine.

Banda haka kasashe da dama sun yi tayin gabatar da duk wani taimako wanda gwamnatin Iran take bukata. Daga Mosco.

Firay ministan kasar Indiya Narendra Mudi ya taya Iran bakin cikin abinda ya faru, sannan yace kasar Indiya ashieye take don gabatar da tallafi.

Sauran kasashen da suka gabatar da ta’aziyya akwai  Japan, Qatar Pakisatn da sauransu, da kuma, Ammar hakim na kasar Iraki,  duk sun yi wa shugaba Pezeskiyan jajen abinda ya faru tare da tayin bada tallafi idan ta bukaci haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments