A safiyar yau Laraba ce aka fara amfani da yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da HKI, kuma shuwagabannin Duniya musamman na kasashen yamma sun yi maraba da hakan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce firay ministan HKI Benyamin Natanyaho ya kira tsagaita wuta, a matsayin na wucin gadi. Sannan kasashe kawayen HKI wadanda suka hada da Amurka, tarayyar Turai da Jamus duk sun bayyana cewa hakan yayi.
Josept Borell ya nuna amincewarsa da tsagaita wutar, ya kuma bukaci a aiwatar da abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Ya kuma kara da cewa da wannan yarjeniyar ana fatan samun sauki a rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.
Jami’in mai kula da harkokin waje na tarayyar ta Turai, Josept Borell ya gabatar da godiyarsa ga gwamnatin kasar Amurka da Faransa wadanda suka yi kokarin ganin an cimmam tsagaita wuta a tsakanin bngrorin biyu.
Gwamnatin kasar Faransa ta ce tana fatan wannan tsagaita wutan zai zama tsagaita wuta na dindin din.