Kasashen Da Suke Kula Da Tsaron Kasar Siriya Zasu Gudanar Da Taro A Birnin Doha Na Kasar Qatar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasashen da suka kula da tsaro da kuma zaman lafiya a kasar Siriya zasu gudanar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasashen da suka kula da tsaro da kuma zaman lafiya a kasar Siriya zasu gudanar da taro a birnin Doha na kasar Qatar don tattauna batun sake bullowar yan ta’adda a arewacin kasar ta Siriya a mako mai zuwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi ministan harkokin waje kasar Iran yana fadar haka a yau Laraba. Ya kumakara da cewa manya-manyan jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Turkiyya zasu halarci taron.

Ministan ya ce, taron Astana na gaba zai gudana ne a birnin Doha na kasar Qatar, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Qatar ba zata halarci taron ba saboda bada cikin kasashen da suke kula da al-amuran tsaro da zaman lafiya a kasar  Siriya da ake kira ‘Taron zaman lafiya na Astana’

Labarin ya kara da cewa kasashen Rasha da Iran dai kawayen kasar Siriya ne, a yayinda kasar Turkiyya kuma take halattar taron a matsayin bangaren da take adawa da gwamnatin kasar Siriya, saboda tana goyon bayan wasu daga cikin kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke yakar gwamnatin kasar ta Siriya.

An kafa kwamitin samar da zaman lafiya ta ‘Astana’ ne a shekara ta 2017 don kawo karshen yakin da gwamnatin kasar Siriya da kawayenta suke fafatawa da kungiyoyin yan ta’adda daban-daban wadanda suke samun goyon bayan kasashen waje tun shekara ta 2011.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments