Kasashen China Da Masar Sun Bukaci Neman Hanyar Warware Matsalolin Gaza, Lebanon Da Siriya

Kasashen Masar da China sun fitar da sanarwar hadin gwiwa dangane da Gaza, Lebanon da Siriya Kasashen Masar da China sun jaddada cewa: Rashin daidaita

Kasashen Masar da China sun fitar da sanarwar hadin gwiwa dangane da Gaza, Lebanon da Siriya

Kasashen Masar da China sun jaddada cewa: Rashin daidaita batun Falasdinu cikin adalci shi ne ginshiki da jigon rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Sanarwar hadin gwiwa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel-Ati da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminisanci ta kasar China kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Pei suka fitar, sun yi kira da a gudanar da shawarwari bisa manyan tsare-tsare, a karshen ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Masar ya kai birnin Beijing na kasar China, don kawo karshen mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kafa kasar Falasdinu mai cikakken yancin kai a kan iyakar da aka shata a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967 kuma babban birninta Gabashin Qudus.

Har ila yau bangarorin biyu sun yi kira da a samar da tsagaita bude wuta nan take a Gaza da kuma janye sojojin mamaya gaba daya daga cikinta, da kuma tabbatar da isar da kayan agajin jin kai cikin aminci da gaggawa da kuma dorewa a dukkan sassan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments