Kasashen China Da EU Sun Maida Martani Kudin Fito Kan Kasar Amurka

Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai

Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu.

Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan da gwamnatin shugaba Trump ta kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama wadanda suka hada da China da kuma kasashen turai EU.

Labarin ya kara da cewa karin kudaden fiton sun shafi motoci da karfe da kuma karfen alminium ne da suke shigo da su daga kasar ta Amurka ne.  Banda haka karin kudaden fiton sun shafi kayakin abinci wadanda suka hada da waken soya, kayan zaki, shinkafa lemun zaki,  almonds,  taba da kuma wasu ababen hawa da kuma Kannan kwalekwale.

Jimillar kayakin da abin ya shafa zai kai Uro billiyon 22.1. sai dai wannan bai kai Euro billiyon 26 wanda gwamnatin Amurka ta karawa kasashen na turai ba.

Labarin ya kammala da cewa sabon kudaden fito na kayakin Amurkan zai fara aiki a ranar talata 15 ga watan Afrilun da muke ciki, wasu kuma 16 ga watan Mayu da kuma wasu a ranar 1 ga watan Decemba karshen wannan shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments