Gwamnatocin kasashen Bahrain sun bayyana anniyarsu ta kyautata danganta a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministocin harkokin wajen kasashen biyu a wata tattaunawa ta wayar tarho sun bayyana anniyarsu ta kyautata dangantaka a tsakanin kasashen biyu bayan katsewat dangantakar Diblomasiyya a tsakaninsu a shekara ta 2016 bayan an kona ofishin jakadancin Saudia take Tehran.
Abdullatif bin Rashid Al-Zayani ministan harkokin wajen kasar Bahrain da farko ya taya Abbas Aragchi sabon ministan harkokin wajen kasar Iran murnan nada shi ministan harkokin wajen kasar Iran.
A nashi bangaren Aragchi ya godewa Al Zayani ta kiransa da kuma gode masa da halattar bikin rantsar da shugaba Pezeskiyan a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa kasashen biyu suna bukatar ci gaba da tattaunawa da kuma fadada dangantaka a tsakaninsu daga inda aka tsaya a bayan.
Ya kuma kara da cewa kyautata dangantaka da kasashe makobta na daga cikin al-amura masu muhimmanci wadanda sabowar gwamnatin kasar Iran ta sa a gaba.
A shekarar da ta gabata ce kasar China ta shiga tsakani ta kuma kyautata dangantakar kasashen Saudiya da Iran wanda kuma kyautata al-amura da dama a yankin kudancin Asiya.