Yemen Ta Sanar Da Nadin Sabon Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar

Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar

Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar Yamen , inda ya gaji Janaral Mohammad Abdulkarim Al-Ghumari wanda yayi shahada a baya bayan nan sakamakon Harin da sojojin HKI suka kaddamar kan kasar ta yamen.

Wannan sabon nadi ya kara tabbatar da karfin guiwa game da jagoranci tsakanin dakarun sojin kasar Yamen a dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da gwagarmaya kan dakarun hadin guiwa da Saudiya ke jagoranta, kuma sun kara jaddada matsayarsu ta gwagwarmayar yanto dukkan yankunan dake karkashin yan mamaya ciki har da birnin Qudus,

Janaral Ali Ghumari yana daya daga cikin mayan kwamandoji masu hazaka acikin dakarun sojin kasar Yamen, yayi shahara wajen bada gudunmawar tsaron kasa da kuma kyakkyawan jagoranci wajen tunkarar kalubalen da suke fuskanta daga kasashen waje,

Jami’an tsaron kasar Yamen sun sha alwashin yin aiki da ababen koyi da kuma tsayin Dakar da ya yayi, da sadaukarwa, kana sun bayyana rashin shahidin a matsayin babbar asara ga kasar, sai dai narasace a  hanyar  neman yanci da kuma jajircewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments