Kasar Sudan Ta Yanke Huldar Jakadancinta Da Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan

Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’

Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi.

Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin gida, ‘yan ta’adda, masu tayar da kayar baya na kungiyar Rapid Support Forces ta dakarun kai daukin gaggawa, kuma masu goyon bayan siyasarsu.

Ya kara da cewa: “Lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tabbatar da rushewar wakilayarta na cikin gida, wanda sojojin Sudan suka fatattake su, sai Hadaddiyar Daular Larabawar ta kara ba da goyon bayanta tare da bayar da karin karfinta wajen baiwa ‘yan tawayen makamai na zamani.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments