Kasar Rwanda Ta Fice Daga Cikin Kungiyar Tattalin Arziki Ta Tsakiyar  Afirka

A daidai lokacin da kungiyar kasashen  tsakiyar Afirka ta tattalin arziki        ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta. Bayanin

A daidai lokacin da kungiyar kasashen  tsakiyar Afirka ta tattalin arziki        ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta.

Bayanin da gwamnatin kasar ta Rwanda ta fitar ya kunshi cewa; Kasar Rwanda tana nuna takaicinta akan yadda kasar DRC take amfani da kungiyar tattalin arziki ta  tsakiyar Afirka a matsayin wani makamin a hannunta.”

Bayanin gwamnatin ta Rwanda ya kara da cewa: Yadda DRC take amfani da wannan kungiyar ya sake fitowa fili a yayin taron kungiyar karo na 26 a Malabo, ta yadda aka kau da kai akan hakkin Rwanda na shugabancin karba-karba,kamar yadda yake a cikin doka ta shida ta kundin kungiyar. Hakan kuma ya faru ne sanadiyyar shiftar DRC ga kungiyar.”

A yayin da aka shirya cewa a shekara mai zuwa kasar ta Rwanda za ta karfi shugabancin kungiyar, jami’an kasar DRC sun ce, ba za su sami halartar taron da za a yi a kasar ta Rwanda ba.

Kasashen biyu dai suna zaman tsami bisa zargin da Kinshasa take yi wa  Kigali na cewa tana goyon bayan kungiyar ‘yan tawaye ta M23.

Yanzu dai kungiyar ta ECCAS tana da mamabobi 11 bayan ficewar kasar Rwanda. Kasashen su ne: Angola, Burundi, Cameroon, Afirka Ta Tsakiya,c, Congo, Gabon, Equatorial Guinea,  Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Rwanda, Sao Tome, sai  tsibirin Principe da  Chad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted