Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; Gwamnati ta amince da a ci gaba da yin wasu dokokin da hana mu’amalar kasuwanci da matsugunan ‘yan share wuri zauna da ba su bisa doka, domin an yi su ne akan kasar Falasdinawa.”
Daga cikin kayayyakin da Majalisar dokokin ta Ireland ta haramta, da akwai ‘ya’yan marmari da itatuwa.
Ministan harkokin wajen Ireland Simon Harris ya fada wa ‘yan jarida cewa, yana fatan ganin matakin da karamar kasarsu ta dauka a kan Isra’ilan ya yi wa sauran kasashen nahiyar turai tasiri su bi sahu.”
Gwamnatin ta Ireland ta sanar da cewa; ta dogara ne da hukuncin kotun duniya ta manyan laifuka wacce ta fitar a watan Yuni na 2024.
A gefe daya kasashe turai da su ka hada Ireland, Spain da Norway sun bayyana aniyarsu ta amincewa da gwamnatin Falasdinu. Ita ma kasar Slovania ta bi sahun wadannan kasashen na turai, yayin da kasar Faransa ta bakin shugabanta Emmanuel Macro ta bayyana cewa; tana Shirin yin furuci da Daular Falasdinu.