Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan fararen hula a Sudan
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da kisan fararen hula a hare-haren da ake kai wa kan asibitoci da cibiyoyin jama’a a Sudan tare da jaddada wajibcin mutunta ka’idoji da dokokin kare hakkin bil’adama a kasar.
Baqa’i” ya yi Allah wadai da kisan mutane a hare-haren da ake kai wa kan fararen hula da ababen more rayuwa, musamman asibitoci da cibiyoyin jama’a a Sudan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana juyayinsa ga wadanda harin baya-bayan nan ya rutsa da su, musamman a birnin El Fasher fadar mulkin Darfur ta Arewa, inda ya jaddada bukatar kiyaye ka’idoji da na dokokin jin kai na kasa da kasa, musamman ka’idar haramta kai hare-hare kan wuraren fararen hula, tare da yin kira da a kawo karshen tashe-tashen hankula da samar da hanyoyin warware rikicin da ke faruwa a Sudan.