Kasar Iran Ta Soki Rahoton Hukumar IAEA Na Baya-Bayan Nan Shirinta Na Makamashin Nukiliya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai. Ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen yammacin duniya ke cutar da martabar wata kungiya ta duniya ta hanyar siyasantar da ayyukanta.

A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar na ci gaba da gudanar da ayyukanta na bin diddigin batutuwan da suka shafi diflomasiyya, yana mai nuni da ziyarar da ministan harkokin wajen Iran ke yi a kasar Masar a halin yanzu, da ziyarar da zai kai kasar Lebanon gobe, da kuma gajeriyar ziyarar ministan harkokin wajen kasar Oman a birnin Tehran. Ya kuma bayyana ziyarar da mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya kai kasar Tajikistan domin halartar taron kasa da kasa, da kuma ziyarar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran yake yi a kasashen Latin Amurka, inda ya jaddada cewa ayyukan sun hada da batun abubuwan dasuka shafi kasashen da na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments