Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Kan Da’awar Kasashen Birtaniya Da Australiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani kan da’awar son zuciya da rashin hujja da kasashen Biritaniya da Australiya suka yi kanta Kakakin ma’aikatar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani kan da’awar son zuciya da rashin hujja da kasashen Biritaniya da Australiya suka yi kanta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Zarge-zargen da suke kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kasashen Birtaniya da Australia suka yi dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba su da tushe ballantana makama, kuma ba su da wani tasiri saboda soki burutsu ne kawai.

A cikin wata sanarwa da Baqa’i ya fitar ya ce: Zarge-zargen da jami’an kasashen biyu suka yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba su da tushe ballantana makama, kuma ba su da wani tasiri. Sannan ya yi kira ga kasashen biyu da su sake duba manufofinsu da suka ci karo da ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma tsoma bakinsu a cikin harkokin cikin gida na kasashe da yankin yammacin Asiya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi ishara da ci gaba da goyon bayan da Birtaniyya da Australiya suke yi na aikata muggan laifuka da kuma hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan yankunan Falasdinu da yammacin Asiya.

Ya kuma yi Allah wadai da matsayinsu na son zuciya dangane da hare-haren tsaron da Iran ta kai wanda ya zo a matsayin mayar da martani ga harin wuce gona da iri da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya, yana mai jaddada cewa: An gudanar da ayyukan tsaron Iran da aka fi sani da “Alkawarin Gaskiya 1 da 2” da suka zo a layi daya tare da ka’idar kariya ta halaltacciyar hanyar doka daidai da dokokin kasa da kasa da Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments