Kasar Iran Ta Jaddada Cewa; Ba Ta Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasashe

Babban sakataren Majalisar Kolin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Ba za su tsoma baki cikin harkokin wata kasa ba domin muradun kansu Babban sakataren

Babban sakataren Majalisar Kolin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Ba za su tsoma baki cikin harkokin wata kasa ba domin muradun kansu

Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian, ya jaddada cewa: Kasancewar Iran a kowace kasa ya ginu ne bisa ka’idoji madaukaka; Yana mai fayyace cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba tsoma baki cikin harkokin wata kasa ba domin biyan bukatun kanta.

Wannan dai ya zo ne a wata hira da kafar yada labaran ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci ta “KHAMENEI.IR” da ta yi da Ahmadiya, dangane da ci gaban da ake samu a yankin Gabas ta Tsakiya na baya-bayan nan, musamman halin da ake ciki a kasar Siriya.

Wannan hirar ta mayar da hankali ne kan mahangar kasantuwar kasar Iran da sharuddan da ake ciki a kasar Siriya da kuma dalilan da suka haddasa ta koma baya musamman bayan rugujewar kungiyar ta’addanci ta Da’ish, da bambance-bambancen da ke tsakanin wannan kungiyar da mayakan da ke mulkin kasar Siriya a yau, da yanayin mu’amalar Iran da wadannan ‘yan bindiga. a cikin shekarun da suka gabata, da yadda take kallon su a yau, da kuma dalilin da ya sa ta yanke shawarar rashin daukan matakin soji cikin abubuwan da suka faru a kasar Siriya na baya-bayan nan, gami da tasirin wadannan abubuwan da suka faru a kan bangaren gwagwarmaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments