Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma wannan yanki shi ne tushen al’amuran duniya da dama, to amma a baya-bayan nan ya fara ne da harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsah wanda kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tsara ta kuma aiwatar da shi, wanda ya zama babbar nasara a kan ‘yan sahayoniya, wannan lamari ne mai muhimmanci.