Iran Ta Ce Tana Hulda Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani

Kasar Iran ta bayyana sake kulluwar hulda da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa

Kasar Iran ta bayyana sake kulluwar hulda da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya sanar da cewa: Wasu kasashe na tuntubar Iran da Amurka a matsayin masu shiga tsakani.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa ya shaidawa tashar Haber Turk ta Turkiyya cewa: Akwai tuntuba tsakanin Iran da Amurka ta wasu kasashe masu shiga tsakani, yana mai cewa: “Wasu kasashe suna hulda da Iran da Amurka, kamar yadda kuka sani, don haka Iran tana tattaunawa da Oman a matsayin mai shiga tsakani.”

Da yake amsa tambaya game da ganawar da kungiyar Tarayyar Turai a Istanbul, ya ce: “Iran ta sake gudanar da wani zagaye na shawarwari tare da kasashen Turai a matakin mataimakan ministoci. An dade ana ci gaba da gudanar da wannan tsari, tana ganawa da tattaunawa kan batutuwa daban-daban kan batun makamashin nukiliya. A taron jiya sun tattauna batutuwan fasaha na batun makamashin nukiliya da kuma batun dage takunkumin da aka sanyawa kasar Iran, kamar yadda Iran din ta jaddada cewa dole ne a samar da duk wani bangare na inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments