Kasar Iran, Da Kasashen Kungiyar BRICS Sun Gudanar Da Taro Kan Harkokin Tsaro A Mosco

An ngudanar da taron harkokin tsaro na kungiyar BRICS karo na 13TH inda wakilai da kasashen Iran da sauran kasashen kungiyar a birnin Mosco a

An ngudanar da taron harkokin tsaro na kungiyar BRICS karo na 13TH inda wakilai da kasashen Iran da sauran kasashen kungiyar a birnin Mosco a ranar Laraba 28 ga watan Mayun da muke ciki.

Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya bayyana cewa babbakan sakataren majalisar tsaro na kasar Iran Ali Akbar Ahmadian da Shugaban Bosnina serb Milorad Dodik da ministan tsaron kasar Korea ta Arewa Ri Chang-dae da kuma da wakilan tsaro daga kasashen duniya fiye da 100 ne suka sami halattan tarom na kwana guda.

A gefen taron a jiya Laraba sakataren majalisar tsaro na kasar Rasah Sergei Shoigu  ya gana da tokwaransa na kasar Iran Ahmadian inda suka tattauna kan al-amura da suka shafe harkokin tsaro tsakanin kasashen biyu.

An gudanar da taron ne daga 27-29 ga watan Mayu da muke ciki sannan wakilai 126 ne suka halarci taron.daga kasashen 104 wadanda suka kasance mambobi a kungiyoyin BRICS,Sco,ASEAN CIS da kuma kasashen kungiyar kasashen Larabawa , Au CSTO da wasu kungiyoyin  kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments