Kasar Habasha Ta Bukaci Kasashen Afirka Su Bunkasa Ciyar Yaki Da Cututtuka CDC Da Kungiyar

Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan

Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan bukatun kiwon lafiya na kasashen nahiyar gaba daya.

Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto Abiy Ahmed yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da daraktan hukumar ta CDC a birnin Adis Ababa a ranar Jumma’an da ta gabata.

An kafa cibiyar yaki da cututtuka ta kungiyar tarayyar Afirka (CDC) ne, a shekara 2016, sannan ta fara aiki a shekara ta 2017 don kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar a nahiyar Afirka.

Gwamnatin kasar China ce ta taimaka aka gina gine-gine cibiyar, aka kuma fara amfani da su a shekara ta 2023.

Abiy yace bunkasa cibiyar ta CDC zai taimakawa kasashen Afirka magance matsalolin kiwon lafiaya da dama a nahiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments