Kasar Faransa Ta Jaddada Aniyarta Ta Amincewa Da Yantacciyar Kasar Falasdinu

Ministan harkokin wajen Faransa ya jaddada aniyar birnin Paris na amincewa da kasar Falasdinu Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tabbatar da aniyar Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa ya jaddada aniyar birnin Paris na amincewa da kasar Falasdinu

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tabbatar da aniyar Faransa na amincewa da kasar Falasdinu, yana mai jaddada cewa wannan amincewa ba zai kasance na bai daya ba, sai dai a matsayin wani bangare na kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe.

Hakan ya zo ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo kasa makonni biyu gabanin taron hadin gwiwa tsakanin Faransa da Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya.

Barrot ya bayyana cewa, makasudin taron shi ne hada kasashe da masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da hukumar Falasdinawa da kasashen Larabawa don ciyar da shirin zaman lafiya gaba. Ya bayyana cewa, Faransa a matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, tana da wani nauyi na musamman a wannan fanni, kuma amincewar da ake sa ran na da nufin kara tabbatar da martabar kasar Falasdinu da samar mata da damammaki.

Barrot ya kuma jaddada muhimmancin tattaunawa kan batun kwance damarar kungiyar Hamas a matsayin wani bangare na duk wani hangen nesa na makomar zirin Gaza bayan yakin. Ya bayyana damuwarsa game da tsarin raba kayan agaji a yankin, wanda ya bayyana a matsayin “tsarin soja”, lura da hargitsi da tashe-tashen hankula da ya haifar, musamman bayan killace yankin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi tun tsawon watan Maris din da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments