Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya nan take, tana mai cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilan tsaro, bayan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai harin Soji a yankin Yammacin Afrika. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar damuwa a yankin Sahel.
Majiyoyin Soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar kasar da Nijeriya, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda daga arewacin Nijeriya na shirin tserewa zuwa cikin Chadi. An ce umarnin ya shafi manyan hanyoyin shiga da fita, musamman ta yankin tafkin Chadi.
Rahotanni sun ce an sanya rundunar Sojin Chadi cikin shirin ko-ta-kwana, tare da tura dakaru da motocin yaki zuwa muhimman hanyoyin da ke hada kasashen biyu. Wannan mataki, in ji majiyoyi, yana nufin hana shige da fice ba bisa ka’ida ba da kuma kare yankunan kan iyaka daga barazanar ta’addanci.
A cikin wata sanarwa, Shugaba Déby ya ce gwamnati ba za ta yarda wata kungiya mai dauke da makamai ko wata kasa ta waje ta yi amfani da kasarsa wajen cimma wani buri ba.