Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran

Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a

Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a lokacin da zaman tankiya ya kara Kamari tsakanin makwabtan guda biyu da ya kai ga rufe iyakokinsu.

A wani yunkuri na kewaye kasar Pakistan  da kuma kaucewa matsalolin da ake samu a iyakarta da Pakistan, kasar Afghanistan ta kara yawan lokacin aikewa da kayayyakinta zuwa tashar jigin ruwa ta chabahar ta kasar iran.

Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afghanistan Abdus salam Jawad Akhundaze Ya ce a tsawon watanni 6 kasuwancinsu da iran ya kai dala biliyan 1.6. fiye da dala biliyan 1 na kayayyakin da take fitarwa ta hanyar Pakistan .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments