Search
Close this search box.

Karin Falasdinawa 35, Sun Yi Shahada A Hare-haren Isra’ila

Bayanai daga Falasdinu na cewa Karin Falasdinawa 35 ne sukayi shahada a sabbin hare haren Isra’ila a Zirin Gaza ranar Litini. Majiyoyin labarai sun ruwaito

Bayanai daga Falasdinu na cewa Karin Falasdinawa 35 ne sukayi shahada a sabbin hare haren Isra’ila a Zirin Gaza ranar Litini.

Majiyoyin labarai sun ruwaito cewa Falasdinawa 9 ne suka yi shahada a wani sabon hari ta sama da gwamnatin Isra’ila ta kai a yammacin birnin Gaza.

Falasdinawa 9 da suka hada da makusanta 6 da masu gadin shahid Isma’il Haniyeh tsohon shugaban ofishin siyasa na Hamas a Gaza ne sukayi shahada a harin da jiragen yakin yahudawan sahyoniya suka kai kan sansanin Shati da ke yammacin wannan birni.

A cewar rahoton, tun da safiyar ranar Litinin, akalla Falasdinawa 35 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.

Bisa sabon rahoton da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya kai 40,139 tun daga ranar 7 ga Oktoban, 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments