Search
Close this search box.

Kanani : Mafarkin Isra’ila Na Kawar Da Gwagwarmayar Falasdinawa Ba Zai Taba Cimma Nasara Ba

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanani ta jaddada cewa “mafarkin ‘yan sahyoniyawa na kawar da gwagwarmayar Falastinawa ba zai taba cimma

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanani ta jaddada cewa “mafarkin ‘yan sahyoniyawa na kawar da gwagwarmayar Falastinawa ba zai taba cimma nasara ba.

Sabanin haka, alama ce ma ta kama hanyar rugujewar gwamnatin sahyoniya baki daya.

A cewarsa, mazauna yankin zirin Gaza wadanda ake zalunta, masu hakuri da juriya sun cika kwanaki 330 na yakin da gwamnatin sahyoniyawan ta shelanta kan zirin.

Ya kara da cewa sama da mazauna wannan wuri 40,000 ne mafi yawansu mata da kananan yara ne suka yi shahada a hannun gwamnatin sahyoniyawa.    

An binne gawarwakin dubban fararen hula, mata, maza, yara da matasa a karkashin baraguzan gine-gine da aka lalata a Gaza.

Kimanin kashi 90% na al’ummar Zirin Gaza sun rasa matsugunansu.

A cewar kungiyoyin kasa da kasa, asibitoci, makarantu, a Gaza duk sun ruguje, wanda aikin sake gina Gaza na iya daukar shekaru masu yawa bayan kawo karshen wannan yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments