Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar

Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar

Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar wuri a matsayin ci gab da nuna kin amincewa da sakamamon zabe.

A can garin Marwa dake a matsayin babban birnin Arewacain kasar,dukkanin harkokin yau da kullum sun tsaya kacokau.

Wani dan kasuwa ya bayyana cewa, rufe kasuwa a wurinsu abu ne mai wahala,amma za su yi ne saboda tsoron kar a kona musu shaguna.

Haka nan kuma ya ce, kasuwar ma ta tsaya cak saboda babu masu saye da suke zuwa.

Da akwai garuruwa da dama da su ka zama kango, saboda kaurewa harkokin yau da kullum da mutane su ka yi a ci gaba da nuna kin yarda da sakamanon zabe.

Wani dan kasuwar mai suna Abdulaziz ya ce; Suna jin tsoron abinda zai faru saboda babu jami’an tsaro da za su ba su kariya.

Wani dalibin jami’a mai suna Gringa Dieudonne ya bayyana cewa gabanin rikicin zabe su 50 ne a cikin ajinsu,amma yanzu su 20 ne kadai suke zama saboda an kauracewa garin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted