Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana.
Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta.
A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa.
Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi mu’amala da sauran kasashe, yana tabbatar da cewa managarsa akan tattaunawa yaudara ce, da kuma son raba Iran da karfin da take da shi, ta hanyar sanya ta ja da baya akan wasu tsare-tsarenta na tsaro.
A cikin kwanakin nan ne dai Donald Trump ya yi batun aikewa da Iran sako yana kiranta zuwa tattaunawa, lamarin da Tehran ta kore.