Kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya bayyana cewa babu kuma wata tattaunawa da HKI, bayan da jakadan Amurka na musamman a kasashen Siriya da Lebanon Thomas Barrach ya isar da sako garesu kan cewa HKI ta ki amincewa da tattaunawa kan ficewarta daga wasu yankunan kasar Leabanon da ta mamaye da kuma shata kan iyakar kasashen biyu.
Kakakin majalisar ya fadawa Jaridar Asharqul Awasat a jiya litinin kan cewa ba abinda ya rage a halin yanzu, sai kasashen da suke kula da tsagaita wutan da aka cimma da ita a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 su yi aikinsu.
Yace su yi aikinsu na tabbatar da cewa HKI ta mutunta yarjeniyar mai lamba 1107 ta MDD wacce ta kawo karshen yaki da ita a watan Nuwamban shekarar da ta gabata. Amma kuma masu lamunin tabbatar da an yi aiki da yarjeniyar wato Amurka da Faransa sun bar ma maganar ta, duk tare da ci gaba da kissan mutanen kudancin Lebanon wanda HKI take yi a duk ranar All..a kudancin kasar.