Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na Amurka, kuma al’ummar Iran sun san halin da ake ciki kuma sun haɗu wuri ɗaya, inda suka samar da garkuwar da ba za a iya ratsawa ba.
Birgediya Janar Ali Mohammad Na’ini, kakakin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci {IRGC}, ya yi jawabi ga mahalarta taron gangamin Ranar Yaƙi da Girman Kai na Duniya a Karaj, yana mai nuna godiyarsa ga kasancewar mutane masu aminci da juyin juya halin Mususlunci na Lardin Alborz a taron gangamin ƙasa a ranar 13 ga Aban (13 ga Nuwamba). Ya bayyana cewa wannan gangamin shi ne na farko tun bayan da aka kakaba wa Iran yaƙin kwanaki 12, ya sake nuna jajircewar jama’a ga taken juyin juya halin, ruhinsu na kalubalantar girman kai, da kuma haɗin kan al’ummar Iran ga kafofin watsa labarai na duniya.
A cikin jawabinsa, yayin bikin tunawa da ranar shahadar shugabar matan duniya Sayyidah Fatima Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), yana mai jaddada cewa ranar 13 ga Nuwamba ba wai kawai tunawa da wani abin da ya faru a baya ba ne ko sake duba wani abu mai sauƙi na tarihi, kuma sanya wannan rana a matsayin “Ranar Ƙasa ta Yaƙi da Girman Kai na Duniya” ba aiki ne kawai na alama ba.