Kafafen Watsa Labarun HKI: Hamas Ta Sami Nasara

Bayan tsagaita wutar yakin Gaza, kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa abinda ya faru wata nasara ne ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas. Kafafen

Bayan tsagaita wutar yakin Gaza, kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa abinda ya faru wata nasara ne ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas.

Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Hamas ta yi nasara a siyasance da kuma ta fuskar soja,ita kuwa Isra’ila ta kasa cimma wadannan manufofin.

Tashar talabijin ta 12 Ta tsara wani rahoto da a ciki ce, Hamas ta hana Isra’ila samun wurin da za ta tsuguna a cikin Gaza, da hakan ya hana ta cimma manufofin yakin.

Har ila yau rahoton ya kara da cewa, Hamas din za ta cigaba da tafiyar da sha’anin mulki a Gaza, alhali Isra’ila ta kasa sauya yanayin yankin.

Shi kuwa Yusi Yusho wanda shi ne mai sharhi akan sha’anin soja a jaridar “Yadiot Ahranot” cewa ya yi ; Bayan watanni 15 na yaki, Benjemine Netanyahu ya ci kasa a siyasance, kuma babban hafsan hafsoshi Laftanar janar Herzi Halevi ya ci kasa a Gaza ta fuskar soja. Don haka babu wata nasara da aka samu akan Hamas a siyasance da kuma ta fuskar soja.”

Tun a farkon shelanta yaki da Benajemine Netanyahu ya yi akan Gaza a 7 ga watan Oktoba 2023,ya yi alkawanin murkushe Hamas ta a fagagen siyasa da kuma soja sannan kuma da kwato fursunonin yaki. Sai dai yanzu bayan watanni 15 babu daya daga cikin wadannan manufofin da su ka tabbata.

Abinda Isra’ila take kira nasara shi ne kashe fararen hula kusan 50,000 da kuma rusa mafi yawancin gidajen yankin na Gaza, saboda fifikon makamai da take da su, da Amurka take ba ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments