Juyayin Ranar Arba’in Na Imam Husaini {a.s} Yana Kara Rusa Makircin Makiya Kasashen Iran Da Iraki

Gagarumin hadin kai da ake samu tsakanin kasashen Iran da Iraki a yayin juyayin ranar Arba’in ta Imam Husaini {a.s} yana rusa makircin makiya Gwamnan

Gagarumin hadin kai da ake samu tsakanin kasashen Iran da Iraki a yayin juyayin ranar Arba’in ta Imam Husaini {a.s} yana rusa makircin makiya

Gwamnan lardin Nasiriyyah na kasar Iraki Murtadha Abboud Al-Ibrahimi ya bayyana cewa: Ana samun nasarar kawar da makirce-makircen makiya hadin kan kasashen Iran da Iraki a yayin juyayin tunawa da ranar Arba’in na Imam Husain {a.s}, yana mai danganta hakan da falalar tattakin ranar Arba’in.

A hirarsa da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, gwamnan lardin Nasiriyya na kasar Iraki ya bayyana cewa: A karon farko tun bayan nada shi gwamnan Nasiriyya watanni 5 da suka gabata, shi da kansa ya jagoranci jerin gwanon masu ziyartan Imam Husaini (a.s) a birnin Nasiriyyah.

Yana mai nuni da cewa, a ziyarar Arba’in ta bana, an yi kokarin baza motocin ceto 100 da suka hada da motocin kai daukin gaggawa, samar da wutar lantarki, da injinan kashe gobara a kan titunan tattakin ranar Arba’in a cikin lardin Nasiriyya kadai, baya ga ware motocin bas-bas 100 maimakon manyan motoci don jigilar baƙi zuwa juyayin Arba’in kyauta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments