Tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.
Ya lashe zaben ne da kashi 56.55 na kuri’un da aka kaɗa a zaben, a yayin da Abokin hamayyarsa, Mahamudu Bawumia ya samu kashi 41.01% na kuri’un da aka kada.
Tun da farko dama, an ruwaito cewa Dokta Mahamudu Bawumia ya kira Mahama, inda ya taya shi murna tare da amincewa da shan kayi.