A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18.
Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka bai wa sunan; Likitan Falasdinawa Husam Abu Saafiyyah.
Har ila yau, hukumar agajin kasar Libya ta tanadi jirgin sama mai saukar angulu domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
Da akwai mutane 20 a cikin wannan jirgin ruwan da su ka likitoci, masu fafutuka da kuma lauyoyi daga Libya da wasu kasashen turai.
Jirgin ruwan na Agaji yana da cikakken goyon bayan al’ummar kasar ta Libya da kuma mahukunta. Daga cikin fitattaun wadanda suke cikin jirgin ruwan da akwai tsohon Fira minista Umar al-Hasi.
Mai Magana da sunan jirign ruwan na Agaji “Nabil al-Sokani ya bayyana cewa; an sami jinkirin tafiyar jirgin ruwan ne na wasu kwanaki saboda rahsin kyawun yanayi da kuma rashin kammaluwar kayan aikin da ake da bukatuwa da su. Amma a halin yanzu an kammala duk wani shiri don haka ta dau hanya.