Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare A Kasar Yemen

Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake

Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake yammacin kasar.

Majiyar tsaron ta Yemen ta ci gaba da cewa; An yi amfani da bama-bamai masu yawa da aka jefa akan wadannan tasoshin jiragen ruwan,kuma fiye da jiragen sama na yaki 10 ne su ka kai harin.

Wata majiyar HKI ta fada wa tashar talabijin din “Kan”  cewa; manufar kai wadannan hare-haren su ne kakaba wa Yemen takunkumi ta ruwa.”

A ranar 6 ga watan nan na Mayu da ake ciki, ma HKI ta kai wani harin akan filin saukar jiragen saman a Sana’a tare da kona jirgen saman kasar da dama.

Ita dai kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen ta sha bayyana cewa ba za ta daina kai wa HKI hare-hare ba har sai idan ta daina kai wa Gaza hari.

Jagoran kungiyar ta “Ansarullah” Sayyid Abdulmalik Al-Husi ya bayyana cewa; Matsayar da Yemen ta dauka na taimakawa Gaza, ba zai fuskanci tawaya ba ko ya ja da baya, zai ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments