Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin.
Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da wakili a cikin kwamitin ttataunawa da ‘yan sahayoniyar da tsohon jakadan kasar Simon Karam yake wakiltarta.
Tashar talabijin din almanar ta ambato ofishin karamar hukumar garin Mahrunah tana yin tir da wannan harin wanda ya rusa wani gida na fararen hula a tsakiyar unguwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa; Kai hari a tsakiyar unguwar fararen hula keta dokokin ‘yan adamtaka na duniya. Kuma abinda ‘yan sahayoniyar suke yi jefa tsoro ne a cikin zukatan mutanen yankin.
Haka nan kuma ya ce; Abokan gaba ba za su iya yin nasarar kashe gwiwar mutanen garin ba,ko kuma su yi tasiri akan jajurcewarsu.
A can Nakura ma, wani karamin jirgin sama maras matuki ya jefa bom a kusa da masu kamun kifi a gabar ruwa.