Jiniyoyin gargadi sun tashi a HKI bayan da sojojin Yemen sun cilla sabbin makamai masu linzami kan HK.
Kafafen yada labarain na HKI sun bayyana cewa makamai na yemen sun haddasa tashin jiniyoyin ne a tsakiyar kasar da kuma yankunan tsakiyar kasar kauam gewayen birnin Qudus.
Majiyar sojojin yemen kuma ta bayyana cewa sun cilla makaman ne don tallafawa falasdinawa a gaza, wadanda HKI take kashewa da yunwa da kuma makamai a ko wace rana.
Labarin ya bayyana cewa dubban dubatan yahudawan sun kideme suna kuma neman inda zasu fake daga boma-boman kasar ta yemen.
Hukumar kwana, kwana, ta HKI wato ‘Israel’s Magen David Adom (MDA)’ bata bada wani rahon jikata da kuma rushe-ruehen da aka samu sanadiyyar faduwar makaman ba.