Jihad Islami: Ranar Quds Dama Ce Ta Hadin Kai Tsakanin Al’umma

Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana

Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana al’ummar musulmi suna sabunta alkawarin da suka yi da Allah dangane da batun Palastinu.

Ranar Kudus tana hada kai tare da karfafa gwagwarmayar Musulunci a yankin.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin bangarori na sun yi imanin cewa,  hanya daya tilo ta kubutar da Kudus da kuma ‘yantar da kasar Falasdinu ita ce goyon bayan Kudus da kuma tinkarar mamaye yankunan Falastinu da hakan ya hada da wannan masallaci mai alfarma da yahudawan sahyuniya suke yi.

Ranar Kudus ta duniya ita ce ranar da ke bayyana dukkan sharrin Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma a wannan rana ne ake daga tutar ‘yanci da barranta daga zalunci, inji shi.

Ya kara da cewa, Wasu daga cikin shugabannin kasashen musulmi suna nuna halin ko-in-kula ga Palastinu da kuma halin da al’ummar Palastinu suke ciki, wanda kuma shirunsu nuna goyon baya ne ga zaluncin yahudawa a kan Falastinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments