Jarirai 70 Sun Yi Shahada A Gaza A Cikin Kwanaki 5 kadai

Hukumar agaji ta Falasdinu ta sanar da cewa a cikin kwanaki biyar kadai da su ka gabata, sojojin HKI sun yi sanadiyyar shahadar jarirai 70

Hukumar agaji ta Falasdinu ta sanar da cewa a cikin kwanaki biyar kadai da su ka gabata, sojojin HKI sun yi sanadiyyar shahadar jarirai 70 a Gaza.

A gefe daya, ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya sanar da cewa a daidai lokacin da aka cika kwanaki 100 da fara kai wa arewacin Gaza munanan hare-hare ta kasa, an sami shahidai da kuma wadanda su ka bace su  5000, sai kuma wadanda su ka jikkata da adadinsu ya kai 9,500, sai kuma wasu 2,600 da  ‘yan sahayoniya su ka kama.

Sanarwar ofishin watsa labarun na gwamnatin Gaza  da jami’in dake tafiyar da shi ya yi taton manema labaru a yau Lahadi ya ce: “  Kwanaki 100 sun cika daga lokacin da sojojin kasa na ‘yan mamaya su ka  fara kawo hari wanda kuma har yanzu yana cigaba, suna kuma yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.”

Har ila yau sanarwar ta ce; A cikin wadannan kwanakin 100,mutanen arewacin Gaza sun fuskanci kisa, rusa gidaje da dukiyarsu da kuma tilasta su yin hijira. Adadin shahidan da  wadanda su ka bace  a wannan tsakanin sun kai 5,000, sai kuma wasu 9500 da su ka jikkata, raunkunan wasu masu hatsari ne matuka. Bugu da kari, ‘yan mamaya sun kama Falasdinawa 2,600 da su ka hada mata da kananan yara.”

Sanarwar ta kuma kara da cewa; Abinda HKI take yi, yana cin karo da dokokin kasa da kasa.

Jami’in watsa labarun ya yi ishara da yadda HKI ya rusa asibitoci da dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya a cikin wannan yankin na arewacin Gaza, tare da cewa; mutanen yankin za su cigaba da jajurcewa da yin tsayin daka domin kare hakkokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments