Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci yabayyana cewa: Iran tana fuskantar makiya da wani bangare na karfinta ne
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana cewa: Makiya sun shiga wannan arangama ne da dukkan karfinsu ne, amma Iran tana fuskantarsu ne da wani bangare na karfinta.
Manjo Janar Hussein Salami ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a wajen taron kasa da kasa na jami’an hulda da jama’a na dakarun kare juyin juya halin Musulunci da daraktocin watsa labarai cewa: Makiya sun shiga wannan arangama ce da dukkan karfinsu, amma har yanzu Iran tana fuskantarsu ne da wani bangare na karfinta. Idan Salami ya yi la’akari da cewa: ‘Yan sahayoniyya sun mayar da hankali ne kan Gaza da Lebanon, amma harkokin siyasarsu sun watsu a duniya.
Manjo Janar Salami ya yi nuni da cewa: A halin yanzu ana ganin shirin siyasa na makiya da ke fuskantar kalubale daga gagarumar turjiyar ‘yan gwagwarmaya a yankin, kuma babu wani karfi da makiya ba su yi amfani da shi ba a fagen yakar ‘yan gwagwarmaya.
Manjo Janar Islami ya kara da cewa: ‘Yan sahayoniyyawan suna kai hari kan duk wani abu da suka samu, suna kai hari kan garuruwan kasar Lebanon, amma sun kasa samun ikon mamaye wani yanki na kudancin Lebanon.
Manjo Janar Salami ya ce: Babbar nasarar da Amurka ta samu a cikin shekara tun bayan kai harin Ambaliyar Al-Aqsa ita ce; Rusa martabarta ta siyasa a duniya.