Janar Salami: Muna  Cikin Shirin fuskantar Yaki A Duk Yadda Ya Zo

Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma

Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo.

Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a hubbaren Imam Ridha ( a.s) ya kuma kara da cewa;  Ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa, idan su ka yi mana barazana, to a shirye muke domin fuskantar kowane irin yaki, a duk yadda ya zo.

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma zargi Amrukawa da cewa su, ba masu cika alkawali ba ne, saboda yadda su ka yi wa Iran barazana da kuma kakaba mata sabbin takunkumai.

Janar Salami ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci ba ta da azamar kera makamin Nukiliya bisa zabinta, ta kuma cire shi daga cikin akidarta ta tsaro.

Kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Muna gargadin abokan gaba akan cewa idan har su ka tafka wani kuskure, to  za a bude musu kofofin jahannama.

Janar Salami ya yi ishara da hare-haren “Wa’adussadiq 1, da na 2 da Iran ta kai wa HKI,sannan ya kara da cewa: Idan har ba za ku iya jurewa makami mai linzami guda daya daga Ansarullah jarumai daga Yemen ba, to yaya za ku yi da daruruwa da kuma dubban makamai masu linzami da za a harbo muku ?

Kwamandan na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ya yi jawabi akan cikar shekara da rasuwar shugaban kasa Ayatullah Ra’isi yana mai cewa; Ya kasance mutum wanda ya tattara soffofi na kamala, don haka ya cancanci yin shahada domin ita ce ta dace da shi.

Haka nan kuma ya yi jinjina ga shahidai irin su Kassim Sulaimani, Isma’ila Haniyyah, Yahya Sinwar, Sayyid Hassan Nasrallah, Safiyuddin, Zahidi, Musawi, ali-Hashim da kuma Rahmati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments