Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar.
A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin kwanaki 12 da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka suka kaddar a kanta. Wannan ci gaban, na nuna bukatar gaggauta sabunta tsarin, da karfafa shi, da kuma bunkasa shirye-shiryen aikin tsaron a dukkanin fagage na sararin samaniya.
Ya kara da cewa, babu shakka, tsaron sararin samaniyar kasar Iran, dole ne ya ci gaba da kasancewa a kan gaba a cikin dukkanin ayyukan tsaro na kasar, sannan kuma dole ne hakn ya kasance daidai da irn barazanar da kasar take fuskanta.
Bugu da kari kan hakan, aiwatar da ayyuka na hadin gwiwa a tsarin tsaron sararin samaniya na kasa, da inganta hadin gwiwa a dukkanin sauran ayyuka na tsaron kasa, wanda hakan ne zai kara tabbatar da haduwar karfin soji da sauran bangarorin tsaro wuri guda.