Janar Bakiri Yace: Sojojin Iran A Shirye Suka Fiye Da Ko Wani Lokaci

Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI

Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a nan birnin Tehran a safiyar yau Litinin.

Ya ce: Halin da sojojin JMI suke ciki yafi na ko wani lokacin kyau, don haka a shirye suke su gudanar da ayyukansu a duk lokacinda bukatar haka ta taso.

Dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kuma, Janar Bakiri ya bayyana cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya rika ya bayyana matsayin JMI dangane da haka.

Kafin haka dai Jagoran ya bayyana cewa Iran a baya ta tattauna da manya-manyan kasashe 6 a duniya daga cikin har da kasar Amurka, an cimma yarjeniyar a tsakanin kasashen mai suna JCPOA, amma shekaru biyu bayan haka shugaban kasar Amurka mai ci, Donal Trump a shekara ta 2018 ya yi watsi da yarjeniyar, ya kuma dorawa Iran sabbin takunkuman tattalin arziki mafi tsanani a kan kasar.

Don haka sake shiga tattaunawa da irin wannan mutum babu mutunci, ba abu ne wanda mai hankali zai amince ba, kuma wulakanci ne ga kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments