Shugaban sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya isa kasar Mali a ranar Asabar a wata ziyarar aiki ta sa’o’i 48.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali Janar Assimi Goïta ne ya tarbe shi a filin jirgin saman Bamako.
Bangarorin biyu na da niyyar karfafa dangantakarsu a fannoni da dama a cewar rahotanni.
A cewar majiyoyin da ke kusa da ganawar da akayi a fadar shugaban kasar Mali, tawagogin biyu sunyi musaya kan batutuwa da dama da suka shafi yankunansu musamman ta bangaren tsaro.
Mali na fuskantar ‘yan tawaye masu ikirari da sunan jihadi, yayin da Sudan, ke fama da ‘yan tawayen FSR.
Bangarorin sun kuma tattauna kan hadin gwiwar soji, inda suka sha alwashin taimakawa juna.
Bamako da Khartoum kuma suna da niyyar yin amfani da damar domin daidaita alakarusu a fagen diflomasiyya.