Jamus:  Wani Dan Kasar Saudiyya Ya Kashe Mutane Ta Hanyar Take Su Da Mota

Kafofin yada labaran Jamus sun rawaito daga mahukuntan jihar Saxony-Anhalt cewa, wata mota ta kutsa cikin taron jama’a a kasuwar Kirsimeti a birnin Magdeburg lamarin

Kafofin yada labaran Jamus sun rawaito daga mahukuntan jihar Saxony-Anhalt cewa, wata mota ta kutsa cikin taron jama’a a kasuwar Kirsimeti a birnin Magdeburg lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 11 tare da jikkatar wasu kimanin 60.

Tashar NTV ta ruwaito cewa, direban motar wanda likita ne dan asalin kasar Saudiyya ya kashe jama’a a kasuwar Kirsimeti a Magdeburg, kuma jami’an tsaro sun samu nasarar kama shi, a cewar rahoton tashar NTV.

Gwamnatin jihar ta bayyana lamarin da cewa aiki ne na  ta’addanci.

Kafofin yada labaran Jamus sun rawaito cewa mutumin da ya kai harin ya shiga kasar Jamus ne yun daga shekara ta 2006, kuma dan asalin kasar Saudiyya da ke aiki a matsayin likita a kasar ta Jamus.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun lokacin faruwar lamarin a daren jiya, an rufe kasuwar baki daya, kuma jami’an tsaro suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa, wannan hari ya haifar da tsoro a cikin zukatan jama’a a daidai lokacin da suke shirye-shiryen bukukuwan kirsimati, tare da yin kira da a kwantar da hankula, kuma a bar jami’an tsaro da su gudanar da aikinsu na bincike da kuma yin abin da ya kamata, ba tare da mutane sun dauki doka a hannunsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments