Jamus: Nahiyar Turai Tana Da Karfin Fuskantar Barazanar Amurka

Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa

Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa dai tana fatan fahimtar juna.

Shugaban gwamnatin kasar ta Jamus; Duk wanda yake son nahiyar turai ta shiga cikin batun zaman lafiya, to dole ne ya yi tarayya da ita cikin daukar matakan da su ka dace.”

Shugaban gwamnatin na kasar Jamus dai yana mayar da martani akan batun kawo karshen yakin Rasha da Ukiraniya ba tare da bai wa kasashen na turai damar bayyana ra’ayinsu akan batun ba.

Dangane da batun kara kudaden fito akan hajar da kasashen turai ke shigarwa Amurka, Olaf Scholz ya ce, Turai tana da karfin da za ya iya fuskantar kowace irin barazana daga Amurka, akan kara kudin fito,’ tare da bayyana fatansa na ganin an kai ga fahimtar juna da zai hana a fada cikin yakin kasuwanci.

Shugaban gwmanatin kasar ta Jamus ya kuma ce; Idan har ya zamana babu  wani zabi a gaban nahiyar turai sai  mayar da martani, to tana da Karfin yin hakan  acikin hadin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments