Kasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Italiya “sun yi maraba” da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza.
A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen suka fitar a birnin Berlin, sun ce shirin idan an aiwatar da shi zai bada damar gaggauta warware mummunan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza.
A yayin taron da suka gudanar ne a ranar Talata data gabata a Masar kasashen Larabawan suka gabatar da wani shiri da zai lakume dalar Amurka Biliyan 53 na sake gina Gaza cikin fiye da shekara biyar inda shirin zai mayar da hankali kan taimakon gaggawa,dawo da ababen more rayuwa da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Shirin na kasashen Larabawa tamakar neman maye gurbin shirin da shugaban Amurka Donald Trump, ya fitar a watan da ya gabatar na karbe iko da zirin Gaza dama tilasta musu hijira zuwa kasashen Masar da Jordan.
Matakin na Trump dai ya fuskanci martini da tofin Allah tsine daga daga Falasdinawa da kasashen Larabawa da kuma gwamnatoci da yawa a duniya, inda sukayi fatali da duk wani shiri na korar mutanen Gaza daga kasarsu ta asali.