Jam’iyyar PPRD Ta yi Tir Da Hukuncin Kisa Da Aka Yankewa Kabila Na Congo

Ƴan ƙasar Congo sun fara mayar da martani kan hukuncin kisa da Babbar Kotun Sojin Ƙasar ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ranar Talata

Ƴan ƙasar Congo sun fara mayar da martani kan hukuncin kisa da Babbar Kotun Sojin Ƙasar ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ranar Talata a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa.

Joseph Kabila mai shekaru 54, ya mulki jamhuriyar Demokradiyar Congo tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019 lokacin da ya mika mulki ga shugaba Felix Tshisekedi da ya gaje shi.

Baya nan cikin kotu, lokacin yanke hukucin a ranar 30 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki, saboda yana can makwabciyarsu Rwanda inda yake zaman gudun hijirar siyasa shekaru biyu da suka gabata.

Yayinda magoya bayan shugaba Tshisekedi ke yabawa matakin, wasu masana siyasa da ƴan adawa na kira da a yi taka-tsan-tsan.

Jam’iyyar PPRD ta tsohon shugaba Kabila dai ta yi tir da mataki. Emmanuel Ramazani Shadary, shine shugaban jam’iyyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted