Jami’in kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas, Osama Hamdan ya ce: Yunkurin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi na kashe tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar wani hari ne kai tsaye kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tsagaita wuta.
Ya kara da cewa a wata hira da aka yi da shi a gidan telebijin, “yunkurin kashe tawagar Hamas hari ne kai tsaye kan shirin shugaba Trump, idan har Isra’ilawa sun amince da Shirin na Trump, to su saurari martanin Hamas, maimakon mayar da martani ta hanyar jefa bam a birnin Doha da wurin taron jami’an kungiyar.”
Hamdan ya yi nuni da cewa, matsayar gwamnatin mamayar Isra’ila, tun bayan kin amsa takardar masu shiga tsakani a ranar 18 ga watan Agusta, a fili take tamkar wani juyin mulki ne ga tsarin sasantawa da kuma manufar cimma matsaya da za ta dakatar da wuce gona da iri kan Gaza da kuma kai ga sakin fursunonin.
Ya ci gaba da cewa, “Muna jiran sakamakon kokari da tuntubar juna da Qatar da Masar suka yi don ganin ko akwai wata niyyar Amurkawa na tursasa Isra’ila ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta karshe.”