Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu wajen wani shiri na sirri kan hada makamin nukiliya a Nijeriya.

A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya fitar a ranar Asabar, jami’ar ta bayyana cewa wannan faifan bidiyon da aka samar ta hanyar na’urar kirkirar bidiyo, karya ne kuma an shirya shi ne don rikita jama’a da bata hakikanin manufar kasar wajen amfani da makamashin nukiliya.

Umar ya jaddada cewa dukkan aiyukan nukiliyar Nijeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin lumana da kuma bin ka’idodin kasa da kasa kamar yarjejeniyar NPT da Pelindaba Treaty, wadda ta haramta samar da makaman nukiliya.

Ya kara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta  jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taba gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments