Kafar watsa laabrun Politico ta fitar da wani rahoto a jiya Talata wanda yake cewa, hukumar bincike ta ‘yan sandan Amurka ta sami bayanan sirri da su ka shafi muhimman matakan siyasa na gwamnatin Amurka da kuma masu alaka da makaman kare dangi.
Majiyar ta ambaci cewa binciken da aka yi a ranar 22 ga watan Ogusta da ya shude ya sami bayanan da aka bayyana a matsayin “Na sirri’ matuka”.
Kafar watsa labarun ta ” Politico” ta kuma ce bayan binciken ofishin bolton da a ka yi, da aka sami na’urar kwamfuta mai cike da bayanan sirri, an kuma kai wani samamen a gidansa dake Jahar Maryland, said ai kuma babu wani bayanai akan nau’oin abubuwan da aka samu a can.
Bugu da kari, ma’aikatar shari’ar kasar ta Amurka tana nazari ko bayanan na sirri da aka samu a gidan Bolton sun shiga karkashin abinda zai iya zama laifi da keta dokokin leken asiri.
Shi dai Bolton ya taba zama mai bai wa shugaban kasar Amurka Donald Trump shawara akan harkokin tsaron kasa a Zangon farko na shugabanci. Sai dai kuma daga baya sun sami sabani a tsakaninsu, wanda ya kai da bude fada a tsakaninsu.
Masu kare Bolton a Amurkan suna bayyana bincikensa da ake yi da cewa, siyasar daukar fansa ce da Trump yake amfani da ita akan wadanda yake fada da su.