Jami’an Tsaron A Nan Iran Sun Kama Yan Kungiyar ISIS Kafin Su Aiwatar Da Hare-Hare

Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk

Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan ta’adda yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa yan ta’addan su 13 daga cikin har da shugabansu, sun kuduri anniyar kai hare-hare a cikin Jama’a su kuma kashe mutane a wasu tarurrukan da aka gudanar a kasar nan.

Labarin ya kara da cewa an kama yan ta’addan na ISIS a biranen Tehran, Qum, Esfahan da kuma Albus. Kuma an kama tare da su kayakin aiki wadanda suka hada da damarar boma bomai na kunan bakin waje da kuma jakunan da ake ratayawa a baya cike da abubuwan Facewa. Kakakin rundunar FARAJA y ace suna dauke da karin bayani nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments